Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Najeriya Sun Kashe 'Yan Bindiga 104 A Jihar Zamfara


'Yan Ta'addan jihar Zamfara
'Yan Ta'addan jihar Zamfara

Shelkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya tace zaratan Jami'anta sun fafata da ‘yan bindigar jihar Zamfara, inda 'yan sandan suka samu nasarra kashe da dama daga cikin su sannan suka kama 85.

Da yake magana a taron manema labari a Abuja, kakakin rundunar ‘yan sandan Mr. Jimoh Moshood, ya ce zaratan ‘yan sandan sun ragargaji ‘yan bindigar a dajin Maga, dake karamar hukumar Birnin Magaji a jihar ta Zamfara.

Kakakin ‘yan sandan na Najeriya, yace sun kashe kimanin ‘yan bindiga dari da hudu, sun kuma rugurguza sansanonin su guda hamsin, kana sun kwato tumaki 500, da shanu 79 daga ‘yan bindigar, amma abin bakin ciki mun rasa dan sandan mu guda daya, kana kuma wasu zaratan ‘yan sanda 12 sun samu raunuka a artabun da mukayi.

Mr. Jimoh yace sun kuma kama ‘yan bindiga guda 85, da kuma manyan bindigogi 27 da kananan bindigogi kirar gida guda hamsin.

An kuma kwato karin shanu dari biyu da saba’in da tara da karin tumaki dari da tara, kuma tuni an mikasu ga masu dabbobin.

Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Hassan Maina Kaina da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:25 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG