ABUJA, NIGERIA - Rukunin masu ziyarar ibadar na biyar a bana daga jihar Lagos da ke dauke da mutum 350 ya dawo gida lafiya bayan ziyartar sassan ibada yayin da a ke barin wuta a yankin Gaza.
Babban sakataren hukumar ziyarar ibadar Reverend Yakubu Pam ya ce kimanin mutum 50 ne daga Lagos ba su samu tafiya ba gabanin dakatar da ziyarar kuma za a koma tafiya da zarar salama ta samu.
Reverend Pam ya kara da cewa ziyarar kan shafi cikin Isra’ila da Jodan don haka masu ibadar su ka takaita ga arewacin Israila inda ba a arangama “wuraren da mu ke tafiya na ta arewa a Israila, kuma Allah ya sa rikici bai same su ba domin Gaza na da nisa daga inda su ke. Sun yi tafiyar su, sun duba wurare da za su yi ibadar su ba damuwa.”
A nasa sharhin kan fitinar ta Yahudawa da Falasdinwa sakataren kungiyar Kiristoci reshen arewa ta tsakiya Simon A.S Dolly ya ce cika alkwarin manzanci ne a littafi mai tsarki da ke bukatar neman sauki daga Allah.
A gefe guda malaman Islama na kira ga samun adalci a matsayin hanyar kawo karshen fitinar ta shekaru aru-aru.
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce fitina ba ta kawo wata riba ga jama’ar da ke zaune a yanki daya “mu na kira ga jama’a a cigaba da tayawa da addu’a don samun zaman lafiya.”
Kamar yanda Saudiyya ke da muhimmanci ga al’ummar Najeriya musamman Musulmi don aikin hajji, hakanan yankunan Israila da Falasdinawa ya ke ga Musulmi, Kirista da ma masu wata akidar da ta saba da wadannan don masallacin Baitul Mukaddas da ke da daraja ga Musulmi, Kirista da Yahudawa.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5