Gwamnatin Najeriya Bata Fara Raba Kudi Ta E-Naira Ba - CBN 

Banban Bankin Najeriya CBN

A daidai lokacin da wani sauti ke yawo a kafafen sada zumunta kan wani shirin gwamnatin Najeriya na raba tallafi ga 'yan kasa ta hanyar asusun E-Naira na babban bankin Najeriya, bankin CBN ya karyata labarin.

Babban Bankin na CBN ya ce bai da masaniya a kan wannan sabon shiri da aka kago ta kafoffin sada zumunta, tare da yin kira ga ‘yan kasar da su yi taka-tsantsan kar wasu miyagu su ci gaba da damfarar su ta wannan hanyar.

Wani matashi ya yi ikirarin cewa shi ne jagoran aiwatar da tsarin asusun na E-Naira na babban bankin Najeriya a yankin Funtua na jihar Katsina a cikin wani sakon sauti, wanda ake ci gaba da yadawa a kafoffin WhatsApp, Facebook da dai sauransu.

Muhammad Hamisu Musa da ke zaman mataimakin darakta a bankin CBN kuma daya daga cikin jami’an da ke kula da aiwatar da tsarin E-Naira na CBN, ya ce akasarin ababen da mutumin ya yi ikirari duk ba gaskiya bane.

E-NAIRA

Masani sha’anin tattalin arziki kuma mai sharhi kan al’amurran yau da kullum, Malam Baba Yusuf, ya ce kamata ya yi babban bankin kasar da saura bankuna su rika daukan kwararran matakai na ganin cewa kulli yaumin ana bibiyar irin wannan yanayi kafin ya taso, ana kuma dakile shi ta hanyar fadakar da mutane.

Idan ana iya tunawa, tun bayan cire tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyar karin farashin kowacce litar mai a baya-bayan nan, majalisar zartaswa ta kasa ta amince da daukar matakan ba da tallafi ga 'yan Najeriya don rage radadin da aka shiga.

Wannan lamarin ne ya kai ga yada jita-jitar cewa bankin gwamnatin tarayyar kasar ya fara raba tallafi ta asusun E-naira na bankin CBN wanda aka musanta daga bisani.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Bata Fara Raba Kudi Ta Asusun E-Nairaa Ba - CBN