NIAMEY, NIGER/MALI - Hukumomin na Mali na zargin wadanan sojoji da shiga kasar ba da saninta ba da nufin hambarar da kanal Assimi Goita daga karaga mulki, zargin da kasar ta Ivory Coast ta yi watsi da shi.
Kakakin gwamnatin rikon kwaryar Mali Kanar Abdoulaye Maiga ya bayyana a kafar television ta ORTM a daren ranar Juma’a cewa, shugaban Mali Kanar Assimi Goita ya yi afuwa wa sojojin nan na Cote d’ivoire 49 bayan da a karshen makon jiya wata kotun kasar ta yanke wa kowanensu hukuncin zaman gidan yarin shekaru 20, bisa zarginsu da shiga kasar ba akan ka’ida ba da nufin tayar da zaune tsaye, yunkurin juyin mulki da wasu tarin laifuka masu nasaba da haddasa rudani.
Matakin kama wadanan sojoji ya haifar da tankiyar diflomasiya a tsakanin kasashen biyu makwaftan juna, a yayin da CEDEAO ta umurci Mali ta gaggauta sakin su ko kuma ta dauki matakin ladabtarwa akanta.
Sai dai a sanarwar da kakakin gwamnatin ya bayar ya ce suna jaddadawa shugaban rikon kungiyar ECOWAS wato shugaban Guinea Bissau Embalo Sissoko cewa, tun a ranar 14 ga watan Janairun 2022 Mali ta fita daga sahun kasashen da ake iya razanawa domin a tun wannan rana kasar ta samu cikakken ‘yancin kanta. Furicin da Nassirou Saidou ke ganinsa tamkar na yaudara.
A ranar 10 ga watan Yulin 2022 ne hukumomin Mali suka cafke sojojin na Cote d’ivoire 49 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman Bamako, saboda zarginsu da shiga kasar ba da izini ba asalin sun je ne da zummar shirya wata makarkashiya a cewar kasar ta Mali, yayin da hukumomin Cote d’ivoire ke cewa dakaru ne da aka tura don ayyukan zaman lafiya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5