A ranar Lahadin nan da ta gabata ne dai wasu ‘yan bindiga su ka kai harin a yankin Ogananibo da ke cikin karamar hukumar Dakina ta jihar Kogi, inda su ka hallaka jama’a da dama tare da jikkata wasu da dama.
Tuni dai gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke yin Allah wadai da wannan hari na aika-aika.
Mr. Kingsley Fanwo shine kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, ya ce gwamnati ta kadu sosai da samun wannan mummunan labari.
Ya ce gwamnatin jihar Kogi tayi Allah wadai da wannan hari kuma tana daukar duk wasu matakai da su ka wajaba na kare rayukka da kuma dukiyar jama’a, kana ya ce tuni gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bada umurnin tura karin jami’an tsaro a yanki.
Da yake karin bayani akan adadin wadanda suka mutu a harin, kwamishinan yada labaran ya ce jami’an tsaro na kan bincike, ba su gama tantancewa ba.
A yanzu haka Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta jihar Kogi ta isa yankin da lamarin ya faru domin ba da agaji ga wadanda su ka jikkata.
Suma dai wasu al’ummar jihar Kogi sun yi Allah wadai da wannan hari a wannan wata na Ramadan da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar Azumi.
Ansa bangaren, Shugaban Kungiyara Izala a jihar Kogi, Alhaji Yahaya Dalladi Musa, ya ce a wannan watan mai alfarma na Ramadan wata ne na zaman lafiya da ibada ba wata ne na tashin hankali ba kuma duk wadanda suka yi wannan abu ba su kyauta ba.
Jihar Kogi dai na fuskantar karin hare-haren ‘yan bindiga dama masu yin garkuwa da mutane, al’amarin da ke matukar bukatar kulawa ta musamman domin shawo kan lamarin.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5