Gwamnatin Kano Da Yan Adaidaita Sahu Sun Cimma Matsaya Kan Rage Kudin Rajista

Ma'aikatan Hukumar Karota

Kasa da mako biyu bayan janye yajin aiki da yan adaidaita sahu suka shiga sakamakon kari a farashin da su ke biya na rijista, gwamnatin jihar kano ta rage kudin rijista a wata matsaya da ta cimma da kungiyar matukan.

Matukan baburan da gwamnatin Jihar Kano dai sun cimma matsaya kan cece -kuce da ya kunno kai bisa ga kari a kudin sabunta rijistar lambar baburan lamarin da ya kai ga matukan suka gudanar da yajin aikin kwana uku da ya kusa tsaida ayyukan sufurin cikin garin Kano cak.

Da maraicen ranar laraba ne bangarorin biyu suka cimma matsayar bayan shafe tsawon sa’o’i 6 ana tattaunawa don samun bakin zaren lamarin kamar yadda wakilinmu a jihar Kano ya shaida.

Taron dai ya sami halartar lauyoyin kungiyar matuka babura Mai Kafa uku da aka fi sani da adaidaita sahu da kuma wakilin hukuma mai kula da zirga-zigar ababen hawa a jihar ta kano da aka fi sani da KAROTA.

Ginin Hukumar Karota

Matsayar da aka cimma ta haifar da da mai ido inda aka rage kudin sabunta rijista daga Naira dubu takwas zuwa Naira dubu 5 kuma kudin yin sabon rajista ya koma Naira dubu 12 sabanin Naira dubu 18 da aka bayyana tun farko.

A bisa wani abu mai kama da gargadi dai, shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba DanAgundi, ya ce duk wanda ya gaza biyan kudin sabunta rijista kan lokaci, zai biya naira dubu 18 da aka kayyade da farko, sai kuma naira dubu 8 ga duk mai bukatar sabunta na sa rijista din.

Idan ana iya tunawa, a makon da ya gabata ne matuka baburan mai kafa uku da aka fi sani da adaidaita sahu suka shiga yajin aikin gamagari a jihar Kano wanda aka shafe kwanaki uku a kai, lamarin da ya saka mazauna jihar cikin tsaka mai wuya wajen zirga-zirgarsu na yau da kullum.

Shugaban Hukumar Karota, Baffa Babba Dan-Agundi

A lokacin da lamarin ya auku dai, ma’aikata sun fi shiga damuwa sakamakon yadda wasunsu ba su da zabi illa su taka da kafa saboda karancin ababen sufuri kamar su motocin bas-bas lamarin da ya dawo da yan acaba wato babura masu kafa biyu.

A bangaren matuka dai, rahotanni sun yi nuni da cewa, an yi asarar akalla naira miliyan uku a kowacce ranar da aka gudanar da yajin aikin lamarin da ya kai jimilar asarar da aka yi ta fuskan tattalin arziki zuwa ga kusan naira biliyan daya.

KAROTA LOGO

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa yajin aiki da aka janye a makon jiya dai Ba shi ne karon farko ba kuma shi ne yajin aiki karo na biyu daga bangaren matukan adaidaita sahun cikin kasa da watanni 12.