Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana kwanaki uku don nuna alhinin mutuwar mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
Mai ba gwamnan jihar Kaduna Nasirsu El-Rufa’i shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adeleke ne ya sanar da hakan a wata sanarwa ranar Litinin 21 ga watan Satumba.
Adeleke ya ce ma’aikatun gwamnati za su yi aiki kamar yadda ka saba a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba, amma ranar Laraba 23 ga watan Satumba za ta zama ranar hutu don tunawa da sarkin.
A cewarsa, “za a sassauto da tutoci a ranakun makokin.”
Sarkin ya rasu ne a asibitin sojan 44 da ke jihar Kaduna ranar Lahadi 20 ga watan Satumba yana da shekaru 84 a duniya.
An yi jana’izar Sarkin a masarautarsa da ke Zaria a kusa da sarakunan masarautar na baya da suka riga mu gidan gaskiya.
Babban limamin masarautar Zazzau, Dalhatu Kasimu ne ya jagoranci sallar jana’izar a fadar masarautar Zazzau da misalin karfe 5:35 na yammacin ranar Lahadi, kuma dubban mutane ne suka halarci taron jana’izar.
Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar harda Malam Nasir El-Rufa’i, da sakataren gwamnatin Kaduna Balarabe Lawal-Abbas, da shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani da wasu mukarraban gwamnati, da kuma manyan sarakunan arewacin kasar.
An nada Alhaji Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau a ranar 15 ga watan Fabarairu a shekarar 1975 kuma ya shafe shekaru 45 yana mukin masarautar kafin mutuwarsa.