Hukumar gidan Rediyon Breeze FM wanda gwamnatin jihar Nasarawa ta rushe tace ta shirya tsaf, na kai gwamnatin gaban kuliya.
A taron manema labarai da darektocin gidan Rediyon suka kira sun bayyana cewa gwamnatin jihar Nasarawa, bata bi matakan da suka dace wajen rushe gidan Rediyon ba.
Mr. Nawani Aboki, shine ya mallaki gidan Rediyon na Breeze FM, yace jama’ar jihar Nasarawa, sunce dole a kai Gwamnan jihar kotu. Ya kara da cewa hukumomin jihar sun tuhumesu cewa yaya suka kafar gidan Rediyon babu izini aka kuma bukacesu da su nemi izini suka kai takardan neman izini ranar juma’a da safe jami’an suka ce suna yajin aiki sai suka koma da yamma sai aka lika takardan rushe gini da safiyar asabar saisuka aiwatar da rushe ginin.
A bangaren gwamnati kuwa kwamishinan yada labarai da raya al’adu a jihar ta Nasarawa, Abdulhamidu Yakubu Kwara, yace takardan mallakar fili da aka baiwa mai gidan Rediyon domin ya gina gidan zama ne ba gidan Rediyo ba kuma idan har yana bukatar gina gidan Rediyo sai ya nemi izini yin haka kuma gwamnati ta tabbatar masa da ita.
Your browser doesn’t support HTML5