Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Mata Na Dada Zama ‘Yan Kwaya


Wata kwayar da jami'an tsaro su ka kama
Wata kwayar da jami'an tsaro su ka kama

Matsalar shaye-shaye tsakanin matasa, musamman mata, ta kunno kai a arewacin Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fama da wasu matsalolin kuma.

Baya ga tunanin yadda za a biya bukatar matasa, wani abin da ke dada damun iyaye a arewacin Najeriya shi ne yadda matasa, musamman ma ‘yan mata, ke dada shiga shan kwaya.


Wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz, ya shirya ma na wannan rahoton:

“Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi, wato NDLEA ke nunawa, matasa masu jini a jika su suka fi fadawa wannan mummunan dabi’a ta shan kwaya.

Baya ga matsalar yan jagaliya, yanzu wata matsalar da ke addabar jama’a ita ce ta shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman tsakanin ‘yan matan da ka iya zama iyaye nan gaba. koda yake hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta sha shirya taruka da gangamin yaki da wannan mugunyar dabi’a, da alamar har yanzu da sauran rina a kaba, kamar yadda ‘yan mayen suka tabbatar.

Masana dai na danganta wannan dabi’ar ne da rashin kulawar iyaye da kuma tarayya da abokanan da basu dace ba.

Alhaji Abdullahi Hassan Zungeru tsohon jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ne wato NDLEA, wanda ya rike jihohi da dama kafin yayi murabus. Ya ce tun da aka soma siyasa kananan yara suka shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi, ciki harda yan mata, batun da ya ce ba zai haifar da da mai ido ba.

To wai ko wace illa shan kwayan ke da ita, musamman ga mata? Malama Salmah Tahir wata malamar jinya a Yola, ta ce:

Baya ga birkita kwakwalwa, kwayar na da wasu munanan illoli. Su kuwa sarakuna iyayen al’umma na fa nuna damuwarsu ce ganin cewa lamarin na kara kazanta. Alh. Muhammad Inuwa Baba Paris, Hakimin Jimeta kuma Dan Isan Adamawa ya ce yanzu haka wadannan matasa na neman zama alakakai ga kansu da kuma al’umma baki daya.’’

Ga wakilinmu Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG