A Janhuriyar Nijar, Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kira manema labarai jiya Talata, inda ta gabatar da wani dan kasar waje, wanda aka kama dauke da miyagun kwayoyi na CFA miliyan 500 mai nauyin kilogiram 3.
Hukumar ‘yan sanda, ta bakin kakakinta Keftin Mainasara Adali Toro, ta ce wajen yinkurin kauce ma na’urar binciken matafiya a filin jirgin sama da kuma yinkurin bayar da cin hanci ga ‘yan sanda ne ya yi sanadin dada tabbatar da cewa wannan mai laifi ne, sannan binciken da ya biyo baya kuma ya tabbatar da hakan.
Haka zalika an kuma gano takardun kudaden Naira da kuma FCA tattare da wannan mutum. Keftin Toro ya kara da cewa binciken ya nuna cewa ba shi kadai yak e tafe da wannan mugunyar harkar ba. Y ace wasu daga cikin mutanen ma an kama su.
Ga wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum