Akasarin ‘yan gudun hijiran da aka koro daga kasar Kamaru ‘yan asalin jihar Borno ne wadanda suka kauracewa matsugunansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram da ya tilasta su fantsama kasashen Kamaru da Chadi dake makwabta da jihar Borno ,kafin daga bisani kasashen biyu suka tasa keyarsu suka jibge su kan iyaka ba tare da an yi wani shirin sake tsugunar da su ba. Lamarin da hukumomin bada agaji a Najeriya suka ce bai dace ba,
A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul’aziz, ‘yan gudun hijiran sun bayyana gamsuwa da matakin da gwamnatin jihar Borno ta dauka na sake masu matsuguni.
A nashi bayanin, Alhaji Aliyu Yarima jami’in tuntuba na jihar Borno, yace, ana kyakkyawan kulawa da ‘yan gudun hijira wadanda yace suna cikin koshin lafiya kuma ana basu abinci isasshe a kalla sau uku a wuni.
Hukumomi da al’umma na ci gaba da bayyana rashin gamsuwa dangane da tasa keyar ‘yan gudun hijirar da gwamnatin kasar Kamaru tayi musamman ganin ziyarar da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kai kasar Kamaru da nufin neman hadin kan kasar a yaki da kungiyar Boko Haram ,da kuma tsugunar da ‘yan gudun hijira.
Ga cikakken rahoton
Your browser doesn’t support HTML5