Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomin jihar Alhaji Usman Zannah ne ya bayyanawa muryar Amurka hakan, ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta yanke shawara domin biyan wasu kananan hukumomi guda 4 albashinsu a shalkwatar kanana hukumomin, kuma nan bada jimawa ba sauran kananan hukumomin zasu koma inda suka fito domin ci gaba da gudanar da harkokin su.
Kusan kananan hukumomi ashirin da biyu cikin ashirin da bakwai ne suka fada cikin hannun ‘ya’yan kungiyar boko haram wadanda daga bisani rundunar sojin Najeriya ta kwato su, kuma yanzu haka an fara gudanar da ayyukan shara da gine ginen gidajen gwamnari a wasu daga cikin kananan hukumomin.
Alhaji Zannah ya yi Karin bayanin cewa, gwamnatin jihar Borno da taimakon kungiyar A T Y Danjuma little support fund, an giggina wasu daga cikin kananan hukumomin, wasu daga ciki kuma gwamnatin jaha ce ta gina tare da taimakon ma’aikatar kananan hukumomi. Ya kara da cewa gwamnan jihar ya ce yakamata jama’ar su koma kauyakunsu domin ci gaba da rayuwa, kuma ya bada umurnin biyan albashi kamar yadda ya kamata.
Mafi yawan wadannan mutane da rikicin boko haram ya daidaita na samun mafaka ne a dakunan zana kokuma rumfunan kwano da suka samarwa kawunansu. Jama’a da dama sun bayyana farin cikin sun a komawa kauyukan nasu, kamar yadda wasu daga ciki suka bayyana rashin matsuguni a matsayayin babban tsaikon da ya hana su komawa kauyakun nasu
Ga rahoton Haruna Dauda Bi’u.
Your browser doesn’t support HTML5