Rikicin na Boko Haram ya tagayyara nakasassu irin su guragu da makafi da kutare da kuma kurame.
Kawo yanzu alkalumma sun nuna cewa akwai nakasassu da suka tagayyara baicin wadanda suka rasa rayukansu.
Rikicin Boko Haram ya sa wasunsu sun rasa dukiyaoyinsu da rayukansu. Wasu ma sun rasa 'ya'yansu da matansu. A rikicin, nakasassu suka fi kowa hasara.
Yayinda hankali ya soma kwantawa hadakar kungiyar nakasassu ta koka game da shakulatin bangarancin da suka ce ana numa masu wajen samun tallafi kamar yadda ake ba sauran al'ummomin dake komawa garuruwansu da aka kwato daga kungiyar Boko Haram.
Kwamred Abubakar Husede shugaban kungiyar nakasassun a jihar Adamawa ya bayyana halin da suke ciki yanzu. Yace kungiyoyi da yawa suna neman tallafi su samu amma ba'a duba na nakasassu.
Yace wai ana shirin kafa wata hukuma ta musamman domin nakasassu, yakamata a ce nakasassu na cikinta domin nakasassu ne suka fi kowa wahala. Kamata yayi a inganta rayuwar nakasassu ta hanyar horas dasu da samar masu ayyukan yi.
Inji Abubakar yakamata a samar masu da ilimi domin inganta rayuwarsu.
Malam Sani Datti kakakin hukumar bada agaji ta NEMA yayi bayani akan kokarin da hukumar ke yi wajen taimakawa nakasassu. Yace a akasarin gaskiya an fi ba nakasassu fifiko wajen bada tallafi saboda halin da suke ciki.
Ga karin bayani