Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Dauki Matakan Soja Kan Tsagerun Niger Delta Idan Ba’a Sasanta Ba


Rundunar sojin Najeriya ta ce zata dauki matakan soja muddin sasancin da ake nema tsakanin gwamnatin kasar da tsagerun Niger Delta ya kasa samun nasara wajan dakatar da kai hare hare da fasa butatan man fetur da cibiyoyin hakar mai dake yankunan.

Babban hafsan rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Tukur Burutai ne ya bayyana haka a baya bayan nan kamar yadda babban kwamandan rundunar soja ta 82, dake birnin Enugu Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana cewa gwamnatin kasar na bin matakan samun sulhu da tsagerun na yankin Niger Delta, amma idan hakan bai yiwu ba, rundunar sojin zata dauki matakin daya dace.

Janar Rabe Abubakar, shine daraktan yada labarai na rundunar sojin Najeriya ya tabbatar da sulhun da gwamnatin kasar k enema da tsagerun na ci gaba da gudana, da kuma matakan da suke dauka.

A kwanakin baya ministan tsaron Najeriya Manjo Mansur Dan Ali, ya kai ziyara a yankin na Niger Delta domin lalubo mafita ga shirin sasantawa da tsagerun yankin na Niger Delta, inda ya gana da shugabannin al’ummomin yankin a jihar Bayelsa domin samun mafita, matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na biyan tsofaffin ‘yan bindigar yankin kudadensu na alawus.

Alhaji Attahiru Bafarawa tsohon gwamnan jihar Sokoto a karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana ra’ayin sa cewa matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na fara biyan tsagerun ya dace domin alheri ne ga kasar baki daya, domin a cewar sa duk wanda yace ayi tashin hankali ba masoyin kasa bane.

Daga karshe Bafarawa ya ce yana kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lallaba da wadannan mutane musamman ganin yadda gwamnatin marigayi ‘Yar adua tayi na shimfida hanyar zaman lafiya domin a cewar sa, arzikin ksar nan na hannun su, koda kuwa za’a koma noma kamar yadda kasar ta samo asali, dole ne sai an bi a hankali har kasar ta samu ta farfado.

Hare haren tsagerun Niger Delta avengers ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Najeriya, ina a kwanakin baya kasar kan hako gangunan danyen mai miliyan biyu da dubu dari hudu a kowace rana, amma yanzu ba’a samun ganga miliyan guda a rana.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.

XS
SM
MD
LG