Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Shugaba Buhari Na Farfado da Tattalin Arziki Zai Dinga Ganawa da Wasu Kwararru


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A cigaba da kokarin farfado da tattalin arzikin Najeriya , wanda yanzu ya komade, kwamitin din da Shugaba Buhari ya kafa dake kula da habakar tattalin arziki yayi taron kiki da kiki da wasu masana ilimin tattalin arziki.

Kwamitin dake karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo da masanan sun zauna ne a fadar shugaban kasa. Sun maida hakanlinsu ne akan dabaru da hanyoyin da za'a bi a farfado da tattalin arzikin kasar cikin gaggawa kafin ya ruguje gaba daya.

Farfasa Osinbajo, mataimakin shugaban kasa ya kara jaddada aniyar Shugaba Buhari na karba da bin duk wasu dabaru da shawarwari da zasu taimaka wajen inganta tattalin arziki, su kara samun ayyukan yi da kawarwa talakawa radadin fatara da talauci cikin gaggawa..

Yayinda yake jawabi a taron, Farfasa Osinbajo yace "zamu cigaba da yin anfani da masana da kwararru da masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki saboda mu dinga auna nasarorin da shawarwari da dabarun da muka yi anfani dasu. Kalubalen nada yawa amma kuma akwai dama mai yawa saboda mun gani karara muna kan hanyar gina tattalin arzikinmu akan tubali mai karfi da zai kirkiro ayyuka ya kuma tabbatar da cigaba da zai yi tasiri akan kowa da kowa", inji Farfasa Osinbajo.

Kwamitin farfado da tattalin arziki zai dinga taro kowane mako kuma zai dingi tattaunawa da 'yankasuwa masu zaman kansu da kwararru daga lokaci zuwa lokaci.

Fitattun masana tattalin arziki da suka kasance a taron da ya ci sa'o'i hudu sun hada da Mr. Bismark Rewane, Mr. Bode Augusto, Farfasa Akpan Ekpo, Dr. Ayo Teriba da Farfasa Badayi Sani.

Abubuwan da suka tattauna sun hada da sake waiwayar tsarin sayar da kudaden waje da yadda ya shafi tattalin arziki da kuma tsara shirin farfado da tattalin arziki na matsakaicin lokaci a shekarun 2017 zuwa 2019.

Mambobin kwamitin da masana tattalin arziki sun bada wasu shawarwari da suke kyautata zaton idan gwamnati tayi anfani dasu za'a samu farfadowar tattalin arzikin. Sun bada shawara a soma kashe kudi kan gine-gine tare da 'yankasuwa domn a tabbar cewa duk wata manufar farfado da tattalin arziki an dorata ne kan muradun jama'a. Sun bada shawarar a kara yawan dala a kasuwar sayar da kudin waje.

XS
SM
MD
LG