Taron wuni uku da Tarayyar Turai ta dau dawainya a yankin Ho na jahar olta a kasar ya horasda masu ruwa da tsaki musamman jami'an shige da fice da 'yan sanda da de sauransu matakan tunkarar bakin haure tare da ceto wadanda a ke safararsu zuwa Ghana.
Binciken baya bayannan ya nuna cewa Ghana na daga cikin wasu kasashen Afurka ta Yamma da ke safarar mutani domin aiwatar da wasu abubuwan da suka saba wa ka'ida, ciki har da karuwanci da barace-barace da wasu ayyukan da su ka fi karfin yara.
Mallam Ibn Yusuf Duranah, mai magana da yawun hukumar shige da fice a jahar arewa maso yamma ta kasar Ghana ya ce a baya bayan nan ma sai da suka ceto wasu kananan yara a hannun masu safararsu
Illahirin bakin hauren su na fitowa ne daga wasu kasashe da ke makwabtaka da Ghana masu fama da rikicin ta'addanci: kamar Najeriya da Nijar da Burkina Faso da dai sauransu.
Marafan Zangon Accra, Mallam Imrana Adamu Bako ya fada wa Muryar Amurka cewa wasu kananan yara da ake fitowa da su daga Nijar suna tsunduma cikin mawuyacin hali sosai.
Wata yar Nijar da ta bukaci da a sakaya sunanta, da ake zargi da safarar kananan yara, ta ce yaran da suke kawowa Ghana marayu ne.
Sarkin Zangon Accra, Alhaji Yahaya Hamisu Bako ya ce a matsayinsu na sarakunan gargajiya suna nasu iya kokarin taimakon samar ma bakin haure sana'a musamman wadanda rikici ya tilasta su ficewa daga kasashensu.
Gwamnatin Ghana dai ta bayyana cewa zata cigaba da maida hankali gurin kare hakkokin bil Adama, musamman wadanda ake safararsu ba bisa kaida ba.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams:
Your browser doesn’t support HTML5