Gwamnatin jihar Borno ta ce ana aikin ruguza wasu gine-ginen Otal a unguwar Galadima dake cikin babban birnin jihar Maiduguri.
Gwamnatin za ta yi hakan ne akan kukan da ke yi na aikata wasu miyagun ayyuka a wuraren da suka hada da gidajen mata dake zaman lalata.
Tun a farkon wanna shekarar gwamnati ta sanar da mutanen dake unguwar cewa za ta rusa gidajen dake wurin kuma ta basu wa'adi su nemi wani matsugunni daban. Gwamnatin ta yi zargin cewa ana aika ayyukan asha a wurin, har ma a wani lokacin a kan yi kisan kai.
Sanadiyar hakan ne ya sa gwamnati ta umurni otal otel da gidajen da ake sayar da barasa da su kwashe tarkacensu su san inda dare ya yi masu. A cewar gwamnati, mafi yawan wadanda suke wurin basu da takardar izinin zama wurin.
Mazauna unguwar sun kira taron manema labarai inda suka kokawa gwamnatin jihar suna neman a tausaya masu. Suna neman a basu dama su mayar da otel otel din gidajen kwana sakamakon rushewar da aka soma yi a yanzu.
Mr Amechi John mai magana da yawun jama'ar da abin ya shafa ya ce suna da otal-otal har guda 21 da gwamnatin ta ce za ta ruguzasu. A cewarsa gwamnati bata karya. Wadanda suka basu wurin basu shaida masu na gwamnati ba ne, saboda haka suna neman alfarma daga gwamnatin ta sassauta masu. Ya ce sun yi gine-ginensu ne da rance daga bankuna ne domin neman abinci.
Ko menene ma zargin da gwamnati ke yi, masu otal din dai roko su keyi.
Makon jiya ne gwamnan jihar Kashim Shettima ya shaidawa Muryar Amurka dalilin daukan wannan matakin.
A cewar gwamnan tun ba yau ba yake samun rahoto akan unguwar Galadima akan irin shashanci da a keyi. Ya ce shi da kansa ya je wurin kuma ya ga abubuwan dake gudana. A unguwar matasa ke shan kayan maye irinsu tramol, wiwi, da kodin da dai sauransu. Saboda haka gwamnan ya ce dole ne su rushe unguwar su gina makarantar 'yan mata a wurin.
Gwamnan ya ce ba zasu tauye hakkin kowa ba. Duk wanda ya cancanta a biyashi diya za'a biyashi.