Gwamnatin kasar Angola ta ce kwanan nan za ta tono tare da yin bison mutunci ma gawar Jonas Savimbi, shahararren dan kasar wanda aka kashe a karshen dadadden yakin basasar kasar.
Dan tawayen, wanda ya rikide ya zama jagoran 'yan adawa, an binne shi ne a wani kauye a 2002, ba tare da irin karamcin da 'yan kasar ta Angola da dama su ke ganin ya cancanta ba, ganin irin tsawon lokacin da ya kwashe ya na gwagwarmaya, da farko a matsayin gwagwarmayar bijirewa danniyar da Turawan mulkin mallaka na Fotugal suka yi, daga bisani kuma a matsayin fafatukar yin watsi da gwamnatin kasar mai bin tafarkin gurguzu.
Hatta wadanda su ka fi sukar gwamnatin - kamar irinsu dan fafatukar kare hakkin dan adam kuma dan jarida Rafael Marques de Morais na cewa wannan matakin da Shugaba Joao Lourenco, wanda ya zama shugaban kasa bara, ya dauka, ya dace,
"Ban da ja kan wannan." abin da Marques ya gaya ma Muryar Amurka kenan. Ya kara da cewa, "Ya na da matukar muhimmanci a yi hakan."