Rahoto na goma sha bakawai akan tattalin arzikin nahiyar Afirka da Bakin Duniya ya fitar, ya bayyana wasu dalilan da suka sa tattalin arzikin ke tafiyar hawainiya duk da hasashen cewa zai samu habaka a shekarun 2019 da 2020.
Wannan tafiyar hawainiyar ta fi shafar kasashe uku mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, wato Najeriya da Angola da Afirka ta Kudu. A yawancin kasashen gabashin nahiyar kuwa, dalin rashin ci gaba ta fuskar noma, ya shafi kasashen saboda karancin ruwa da yawan kudin ruwa da suke fama dashi.
Wani masanin tattalin arziki na Bankin Duniya dake kula da nahiyar Afirka ya ce rahoto na 17 da bankin ya fitar, ya maida hankali akan abubuwa uku da zasu kaiga bunkasar tattalin arziki a Afirka-kudu da hamada. Ya ce wajibi ne gwamnatocin Afirka su tashi tsaye domin habaka tattalin arzikin su domin su yi tafiya da duniya.
A halin da ake ciki yanzu, Afirka zata bunkasa ne kawai da kashi 3.1 a shekarar 2018 sannan a shekarar 2019 zuwa 2020 tattalin arzikin zai habaka da 3.6 ne kawai yayinda a duniya gaba daya za'a samu habaka da ta kai 5.00.
Kasashen Afirka dole su maida hankali akan tsadar ko yawan kudin ruwa kan basussuka da suke karbowa a kowace shekara.
Ywana basussuka suna marukar illa ga kasashen Afirka.
Ga rahoton Ridwan Abbas da karin bayani
Facebook Forum