Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Angola ta yi sabon shugaba a karon farko cikin shekaru talatin da takwas


Sabon shugaban kasar Angola Lourenco bayan an rantsar da shi
Sabon shugaban kasar Angola Lourenco bayan an rantsar da shi

An rantsar da Joao Lourenco a matsayin sabon shugaban kasar Angola, a karon farko cikin shekaru talatin da takwas

Talata aka rantsar da Joao Lourenco a matsayin sabon shugaban kasar Angola. Kasar mai arzikin mai, ta samu sabon shugaba a karon farko cikin shekaru talatin da takwas.

An rantsar da sabon shugaban ne a Luanda baban birnin kasar, a wani bikin daya samu halarcin dubban yan kasar, da kusan shugabanin kasashe talatin da kuma tsohon shugaban kasar Hose Edwardo Dush Santush.

Bayan da yayi rantsuwar kama aiki, tsohon shugaba Dush Santus ya mikawa sabon shugaban kasa , abun wuyan shugabanci dake zama alamar mika mulki

Ana rade raden cewa tsohon shugaban kasar Dush Santush dan shekara saba’in da biyar da haihuwa bashi da cikakken lafiya. Ya yanke shawarar cewa ba zai tsaya takara ba a bana, matakin da ya baiwa jam’iyar MPLA, wadda take jan ragamar mulkin kasar damar tsayar da tsohon Ministan harkokin waje dan takarar ta na shugaban kasa.

Kamar yadda suka yi alkawari babar jam’iyar masu hamaiya ta UNITA da kawayenta sun kauracewa bikin rantsar da sabon shugaban kasar.

Jam’iyun sun kalubalancin sakamakon zaben da aka yi a watan Augusta ba tare da samun nasara ba.

A jawabin daya gabatar na tsawon mintoci arba’in da bakwai, sabon shugaban na Angola Louremca yayi alkawrin cika alkawain da yayi a lokcin yakin neman zabe na yaki da cin hanci da rashawa daya ce yayi katutu a ma’aikatun gwanatin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG