Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Angola Na Zargin Dan Tsohon Shugaban Kasar Da Wawure $500m


José Eduardo dos Santos , tsohon shugaban kasa kuma mahaifin Filomeno dos Santos wanda aka zarga da wawure $500m daga babban bankin kasar
José Eduardo dos Santos , tsohon shugaban kasa kuma mahaifin Filomeno dos Santos wanda aka zarga da wawure $500m daga babban bankin kasar

Mahukuntan kasar Angol sun hana dan tsohon shugaban kasar da gwamnan babban bankin kasar barin kasar

Hukumomin kasar Angola sun tuhumi Jose Filomeno dos Santos, dan tsohon shugaban kasar Edwardo de Santos, da aikata rashin gaskiya kan zargin tura dalar Amurka miliyan 500 daga babban bankin kasar zuwa Ingila.

Hukumomin kasar sun hana Jose barin kasar, haka nan tuhumar ta shafi tsohon gwamnan babban bankin kasar, shima an hana shi yin balaguro domin aiwatar da binciken kwakwaf akan lamarin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG