Gwamnatin Amurka ta fara tambayar baki masu shiga kasar ziyara su bayyana kafofin sada zumuncin da suke amfani da su, a wani kokari na gano ‘yan ta’adda ko masu shirin aikata ta’addanci.
Tun a makon jiya, bakin da suke shigowa nan Amurka daga kasashen da basa bukatar visa, aka fara tambayarsu irin kafofin sada zumunta da suke amfani da su, da kuma sunayen da suke amfani da su a kafofin.
Duk da yake ba dole ne sai mutum ya bayar da bayanansa ba, jami’ai sunce ba zasu hana mutum shiga Amurka ba a dalilin ‘kin bada wannan bayanai.
Wannan yunkuri dai ya janyo suka daga wasu cibiyoyi dake kare ‘yancin walwalar jama’a da dimokaradiyya da kuma kamfanonin fasaha. Matakin da suke cewa ya sabawa ‘yancin magana da bayyana ra’ayi.
Your browser doesn’t support HTML5