Rundunar ‘yan Sandan jihar Neja, ta cafke wani makaho da ake zargi da luwadi,shi da wannan makaho mai suna Idris Usman, ana zarginsa da yaudarar wasu yara maza biyu ne da kudi domin yayi lalata dasu.
Makahon mai shekaru sittin (60) wanda aka fi sani da sunan Bagobiri, an cafke shine bayan da daya daga cikin yaran Zangina, mai shekaru goma sha biyu, ya fara rashin lafiya, kais hi asibiti, ke da wuya sai likitoci, suka gano cewa harbu da kwayoyin cutar a duburarsa.
Da ‘yan Sanda suka binciki yaron baya da ya amsa tambayoyi sai yace Bagobiri, yak an basu Naira hamsin (50) ko Naira dari (100) duk lokacin da yayi lalata dasu, dashi da abokinsa Mustapha, mai shekaru goma. Kuma yace an samu tsawon shekara daya yana yin lalata dasu.
Da take tabbatar da afkuwar lamarin daraktan yancin yara ta jihar Mairam Kolo, tace wannan batu ne na yin luwadi da yara kanana wanda doka jihar tayi tanajin tsare duk wanda ya aikata irin wannan a gidan yari na tsawon rayuwa, wanda ita kuma hukumar dake kula da yancin yara ta gidaya shekaru goma sha hudu a gidan yari da kuma biyan diyya ga duk wanda irin haka ya faru gareshi.