Gwamnatin Adamawa Ta Musanta Zargin Korar ‘Yan Gudun Hijira

ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da aka rufe sansaninsu

Gwamnatin jihar Adamawan dake cikin jihohi uku da rikicin Boko Haram yafi shafa, ta musanta zargin cewa ta soma korar yan gudun hijiran dake jihar.

Gwamantin ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo, ta ce ta sauyawa yan gudun hijiran Damare matsuguni ne, don sake farfado da sansanin yan yiwa kasa hidima ne kamar yadda aka saba kafin barkewar rikicin Boko Haram, fiye da shekaru bakwai.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ita ke kula da sansanonin da aka tanadar, kuma kamar yadda jami’in hukumar mai kula da jihohin Adamawa da Taraba Sa’ad Bello ya bayyana, tuni suka karbi wadanda aka sauyawa matsugunin a sansanin Malkohi.

Wadannan yan gudun hijiran da aka sauyawa matsugunin sun yaba da yadda suka tarar da sabon wurin koda yake tuni wasunsu suka tare a cikin gari.

Baya ma ga rayukan da suka salwanta, rikicin Boko Haram ya tilastawa wasu dubban jama’a gudun hijira a ciki da wajen Najeriya, koda yake kawo yanzu wasu tuni suka koma, biyo bayan kwanciyar hankalin da aka samu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Adamawa Ta Musanta Zargin Korar ‘Yan Gudun Hijira - 3'51"