A karon farko, yau an hada ‘yan matan Chikbok din nan 82 da aka sako daga hannun kungiyar Boko Haram tareda iyayensu a wani shgaali da aka yi a Abuja, babban birnin Nigeria din.
Yaran na cikin dalibbai 276 da akia sace daga makarantarsu a shekarar 2014. Daga baya aka sako su wadannan na baya-bayan, bayan musayar da hukumomi suka yi da ‘yan Boko Haram din, suka maida musu wasu mutanensu da aka kama, su kuma suka sako ‘yan matan.
A cikin watan Oktoba ne aka sako ‘yan matan 21, wasunsu kuma suka gudu da kansu.
Sai dai har yanzu akwai ‘yan mata fiyeda 100 da ke ci gaba da ake ci gaba da rikewa, koda yake gwamnati tace tana ci gaba da kokarin neman sauran ‘yanmatan.
Facebook Forum