Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Musulmi Su Kasancewa Masu Zaman Lafiya Da Rikon Amana


Tausayawa juna da taimakon da yakamata tsakanin al'uma zai rage rashi da zaman kunci a l'uma.

Yayin da ya rage kwanaki a fara azumin watan Ramadan an bukaci masu hannu da shuni da su taimakawa mabukata sailin nan kuma ‘yan kasuwa su tausayawa jama’a su rage farashin kayayyaki.

Wani basaraken gargajiya Galadiman Akinyele, kuma Sarkin Yamman Keffi, Alhaji Hussaini Abubakar, ne ya furta haka a wata tattaunawa da muryar Amurka, a birnin Ibadan na jihar Oyo, a Najeriya.

Ya kuwa yi kira ga al’umar Musulmi, da ayi amfani da watan Ramadan mai daraja a yiwa Najeriya da shugabaninta adu’a da kuma kasancewa al’uma masu zaman lafiya da rikon amana, domin kasa ta samu ci gaba mai torewa.

Alhaji Hussaini Abubakar, yayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yunkuro akan batu ma’adanai da kuma masana’antun da suka durkushen a jihohi daban daban masamman wadanda ke Kaduna domin bukasa tattalin arzikin kasar da kuma samawa matasa aikin yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG