PLATEAU, NIGERIA - Gwamnatin jihar Filato ta bukaci hukumomin da ke da hurumin kamo wadanda ke da hannu kan kashe-kashen da aka yi a karamar hukumar Mangu da kewaye, su bayyana wadanada suka kama don hukuntasu.
Gwamnan ya kuma yi alkwarin tallafawa dubban jama’a dake gudun hijira.
Matasa da mata daga sassa daban-daban na jihar Filato sun taru a wuri guda don nuna alhininsu kan kashe-kashen da kuma bayyana bukatar gwamnati ta kawo karshen hare-haren da ake kaiwa kan jama’a.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono ya bukaci a samar musu da tsaro.
Shima Kansila mai wakiltar Mangu Ward one, Kabiru Iliyasu yayi kira wa zababbun ‘yan majalisu su duba batun tsaro da idon basira.
Mutane fiye da dari ne bayanai ke nuna sun hallaka a hare-hare da aka kai a karamar hukumar Mangu cikin ‘yan kwanakin nan, yayinda dabbobi da dama suka salwanta, gidaje masu tarin yawa da wuraren ibada aka kona, dubban mata da yara da tsofoffi da maza ke gudun hijira suke kuma bukatar agajin gaggawa.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5