Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bada Umarnin A Kashe Yan Bindiga Masu Garkuwa Da Mutane 

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi)

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya umarci al’ummomin  jihar da su kashe  masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’addan da suke yankunansu. Gwamnan yayi wannan ikrari ne a garin Rimi dake yankin karamar hukumar Alkaleri.

BAUCHI, NIGERIA - Gwamnan ya bada umarnin ne a lokacin da yake jajanta musu dangane da kashe mutanen su fiye da goma sha biyu da wassu ‘yan bindiga sukayi.

Yan Bindiga

Daga cikin wadanda suka rufawa Gwamnan baya don jajanta wa mutanen sun hada da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi Aminu Alhassan, inda suka ziyarci kauyukan Rimi, Mansur da kuma Yelwan Duguri.

A jawabinsa ga al’ummomin kauyukan CP, Aminu Alhassan, ya ce shi da sauran abokan aikinsa jami’an tsaro ne suka fatattaki ‘yan bindigan.

Yan Bindiga

A nasa jawabin Gwamnan Bauchi Senata Bala Abdulkadir Muhammed, ya jinjinawa jami’an tsaro game da kokarin da suka yi, kuma ya bada tabbacin bada tallafi wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, sannan ya bada umurnin a kashe duk wani ‘dan ta’adda da akayi ido biyu dashi.

Shugaban karamar hukumar Alkaleri na riko, Comrade Ibrahim Bala Mahmood, ya bayyana jin dadi dangane da ziyarar da Gwamnan da kuma tawagarsa suka kawo don jajanta musu game da abin da ya same su.

Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bada Umarnin A Kashe ‘Yan Ta’adda Da Masu Garkuwa Da Mutane .mp3