Gwamnan Filato Ya Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Kauyen Ancha

Gwamnan Filato Simon Lalong (Facebook/PLSG)

Jihar Filato ta sha fama da matsalolin hare-haren da kan kai ga asarara rayuka da dumbin dukiyoyi.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya yi tir da wani sabon hari da wassu ‘yan bindiga suka kai kauyen Ancha a karamar hukumar Bassa, suka kashe mutane da dama, suka kuma lalata dukiya.

Gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun kamo maharan ko ta wani hali.

Gwamna Lalong ya bukaci kwamandan runduna ta 3 da kwamandan ‘Operation Safe Haven’ tare da kwamishinan ‘yan sanda, da ma’aikatan jihar, Operation Rainbow da su yi amfani bayanan sirri wajen kama wadanda suka aikata laifin.

Kazalika Lalong ya bukaci a yi amfani da bayanan wadanda suka tsira da rayukansu da kuma wasu majiyoyi gano wadanda suka yi wannan aika-aika.

A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kame wadansu da take zargi da yin manyan laifuka da suka hada da yin garkuwa da mutane, kisan kai, ‘yan kungiyar asiri, masu fashi da makami da sauransu.