Gwamnatin jahar Filato ta umurci jami’an tsaro su bankado ‘yan bindigar da suka kashe mutane da wayewar garin yau Jumma’a, a kauyen Ta’agbe da ke karamar hukumar Bassa, don a hukunta su.
Da wayewar garin yau Jumma’a ne dai wassu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a kauyen na Ta’agbe, da ke kan iyakar jahar Filato da Kaduna, suka kashe mutane suka kuma kone gidaje da kayan amfanin gona.
Mai magana da yawun kungiyar raya kabilar Irigwe, Davidson Malison ya ce sun binne gawarwaki guda goma.
A gefe guda kuwa, shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore a jahar Filato, Umar Dakare ya ce ba Fulani ne suka aikata kisan ba.
Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da hukumar inganta zaman lafiya a jihar da su tantance aukuwar lamarin don tallafa wa wadanda iftila’in ya abka musu.
Saurari rahoton Zainab Babaji: