Gwamnan ya yi yabon ne lokacin da ita hukumar UNHCR ta bada kayan tallafin wa wasu a garin Konduga da suka koma suna kokarin sake gina muhallansu.
Yace taimakon mutanen da basu da karfi su kimanin dubu biyu ba karamin taimako ba ne. Yace sun ji dadin irin taimakon. Dubu talatin da aka baiwa mutane dari uku a garin Konduga kadai da kuma kayan gini saboda haka gwamnan ya sake mika godiyarsa ga UNHCR da ma'aikatar gine-gine saboda adalcin da ma'aikatan suka nuna.
Shugaban hukumar ta UNHCR yace taimakon kankani ne amma na nuna murnarsu saboda kokarin da gwamnatin jihar ta keyi na sake gina jihar Borno.
Kwamishanan gine-gine na jihar yace akwai mutane dari biyar da suka anfana da tallafin UNHCR, daga karamar hukumar Gwoza, dari uku daga Konduga dari uku daga Mafa dari biyar daga Dikuwa dari biyar daga Damboa sai kuma dari daga karamar hukumar Bama.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5