Yayinda gwamnan jihar Kashim Shettima yake gabatarwa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekara mai zuwa, ya karyata zargin ma'aikatan tare da cewa kawo yanzu ko kwandala ma'aikata basa bin gwamnatinsa.
Yace daga watan Yuni na wannan shekarar jihar nada ma'aikata 27,366 da suka hada da malamai da dalibai. Yace kawo yanzu an tantane ma'aikata 18,366 kuma an biyasu. Yace akwai ma'aikata 3,441da suke da matsaloli daban daban. A cewarsa wasu tsiraru ne kawai ke kokarin tada hankulan mutane.
Inji gwamnan duk cikin manyan makarantun gaba da sakandare dake Najeriya jihar Borno ce tafi biyan albashi mai tsoka. Yace idan ba gaskiya ya fada ba a fito a karyatashi.
Gwamna Shettima yace kowane wata gwamnati na biyan Ramat Poly nera miliyan 133. Yace ma'aikatan Ramat Poly suna karban albashin da ya dace tare da sauran alawus alawus. Gwamnan yace yana kokarin ya yi abun da ya kamata komenene ma zai faru.
Amma kungiyar malaman Ramat Poly tace basu gamsu ba saboda gwamnatin tana da wata manufa daban. Shugabansu Baba Shuwa Gwani yace ashirye suke su tari aradu da ka saboda sun san akwai wadanda ba'a biyansu albashi na wata shida ko bakwai ba a cikinsu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.