Idan ba'a manta ba tun watan Afirilun shekarar 2014 ne 'yan kungiyar Boko Haram suka bi dare zuwa makarantar 'yan mata dake Chibok suka sacesu kuma tun daga lokacin ake fafutikar cetosu.
Yayinda yake mika wa gwamnan Borno Alhaji Kashim Shettima yarinyar da jaririnta yace sun tabbatar Rakiya na cikin 'yan mantan da 'yan Boko Haram suka sace kusan shekaru uku da suka gabata. Janar Irabor yace baicin yarinyar sojojinsa sun samu nasara kututar da wasu mata da dama tare da kananan yara da tsoffi.
Gwamna Shettima ya nuna farin cikinsa bisa ga kutubar da wannan yarinya Rakiya tare da fatan sauran ma za'a ganosu nan ba da dadewa ba.
Malam Yakubu Kiki shugaban iyayen 'yan matan da aka sace ya tabbatar Rakiya na cikin wadanda aka sace kuma ya ce sunanta na ainihi shi ne Rakiya Gali Mulima.
Wata Malama Rebecca daya daga cikin 'yan matan da aka sace amma aka sakota cikin 'yan mata 21 kuma 'yar uwar Rakiya sun rungumi juna tare da yin hawaye.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.