Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Mika Kansu Ga Rundunar Sojoji A Borno


Wasu cikin 'yan Boko Haram da suka mika kansu da kansu ga rundunar sojojin Maiduguri a Borno
Wasu cikin 'yan Boko Haram da suka mika kansu da kansu ga rundunar sojojin Maiduguri a Borno

Rundunar sojojin Najeriya dake Maiduguri jihar Borno ta gabatar da wasu mutane guda goma ga manema labarai da tace 'yan kungiyar Boko Haram ne da suka mika kansu da kansu da da makamansu sunan sun tuba

Kwamandan rundunar Janar Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai cewa 'yan ta'adan da suka mika kansu da kansu sun mika makamansu bayan sun yi nadama.

Yace nadamar da suka yi ya sa suka karbesu da hanu biyu kuma duk wanda zai ajiye makaminsa ashirye suke su karbeshi.

Wasu cikin 'yan Boko Haram da suka mika kansu da kansu
Wasu cikin 'yan Boko Haram da suka mika kansu da kansu

Rundunar ta ba mutane ukku cikin goman damar yiwa 'yan jarida bayani. Sun tabbatarwa 'yan jarida cewa lallai su 'yan Boko Haram ne da yanzu suka mika kai tare da yin nadama.

Mutanen sun bayyana cewa rayuwarsu ta jeji ba rayuwa ba ce. Sun ba gwamnati da 'yan Najeriya hakuri. Daya daga cikinsu baya Hausa yayi turanci ne. Yace sunansa Joseph David amma kungiyar ta sa masa suna Ibrahim Alechi. Ya yaba da yadda sojojin suka kula dashi lamarin da ya bashi mamaki domin bai yi tsammanin haka ba. Ya godewa Ubangiji da sojojin. Ya kira wadanda suke daji da su fito suma su mika kansu domin ba za'a kashesu ba.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG