Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya kafa wani kwami mai karfi da zai binciki kungiyoyi masu zaman kansu ko NGO dake samar da agajin gaggawa lokacin rikicin Boko Haram.
Manufar binciken shi ne ya gano yadda suke gudanar da ayyukansu ko domin Allah ne kuma da gaske suke yi saboda taimakawa al'ummar Borno ko kuma sun shigo ne domin biyan bukatun kansu?.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude taron masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro a jihar wadanda ya hada da rundunar sojin kasa da 'yan sanda da DSS da wakilan jami'an tsaro dake aiki a jihar.
A cewar gwamnan daukan matakin ya zama dole domin tabbatar cewa an sa ido kan yadda kungiyoyin masu zaman kansu ke aiki a jihar.
Wannan shi ne karon farko da gwamnan ya bari 'yan jarida suka shiga inda yake taron tare da yin jawabin. Amma bayan jawabinsa an sallami 'yan jarida kana jami'an tsaron suka ci gaba da taronsu da gwamnan.
Inji gwamnan jami'an tsaro sun riga sun shawo kan 'yan ta'addan kuma abun da su keyi yanzu tamkar shure-shure ne wanda kuma baya hana mutuwa.
A saurari rahoton Haruna Dauda da cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5