Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sallami sakataren kula da harkokin tsofaffin sojoji
Sauye sauyen shugaban Amurka Donald Trump, na ma’aikatansa ya ci gaba a Jiya Laraba inda ya kori sakataren kula da harkokin tsofaffin sojoji David Shulkin.
Shugaba Trump, ya rubuta a shafin sa na tweeter cewa, “Ina farin cikin sanarwar cewa na yi niyyar in zabi mai girma Admiral Ronny Jackson, a matsayin sabon sakataren kula da al’amurran tsofaffin sojoji.”
Yanzu dai Jackson, wanda shine Likitan dake kula da lafiyar shugaba Trump, kuma wanda ya duba lafiyar sa a kwanan nan, shine zai maye gurbin tsohon sakataren kula da tsofaffin sojojin.
Tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama, ne ya nada Jackson a shekarar 2013 kuma Donald Trump, ya ci gaba da aiki da shi.