Griezmann Ya Sake Komawa Atletico Madrid

Antoine Griezmann

Barcelona har ila yau ta sayar da dan wasan tsakiyanta Ilaix Moriba ga kungiyar RB Leipzig akan kudi euro miliyan 16.

A wani lamari na ba-zata, dan wasan Barcelona Antoine Griezmann ya koma Atletico Madrid a matsayin dan wasan aro na tsawon kakar wasa bisa yarjejeniyar za a mayar da komen na dindindin akan kudi euro miliyan 40.

Dan asalin Faransa, Griezmann ya koma Barcelona ne a shekarar 2019 akan kudi euro miliyan 120.

Sai dai masu sharhi na cewa ya gaza tabuka wani abin a-zo-a-gani, inda ya ci kwallaye 22 cikin wasanni 74 da ya bugawa Barcelona a gasar La Liga.

Griezmann ya kwashe kakar wasanni biyar a Atletico bayan da ya bugawa Real Sociedad inda tauraronsa ya fi haskawa, inda ya ci kwallaye 94 a wasanni 180.

A wani lamari makamancin wannan, Barcelona ta sayar da dan wasan tsakiyanta Ilaix Moriba ga kungiyar RB Leipzig akan kudi euro miliyan 16 inda za a kara miliyan 6 a nan gaba.

Cikin makonnin da suka gabata kungiyar ta saki dan wasanta Lionel Messi wanda ya koma PSG bayan kwashe shekaru da dama yana murzawa kungiyar kwallo.

Rahotanni sun ce Barcelonan ta sauya kwantiragin wasu ‘yan wasanta da dama inda aka rage kudaden da ake biyansu.