GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Bayani Kan Batun Cin Zarafin Yaro Kurma-Kashi Na Daya-Yuli,04, 2019

Grace Alheri Abdu

Yau shirin Domin Iyali zai waiwayi wani batu da ya dauki hankalin al'umma farkon shekarar nan da ya shafi wani karamin yaro kurma da iyayenshi ke zargin an yi mashi fyade da gasa mashi akuba a makarantar kurame ta gwamnati dake Kuje, Abuja, zargin da ake samu bayanai masu karo da juna tsakanin jami'an asibiti, da 'yan sanda da kuma ma'aikatar ilimi ta tarayya.

Zamu yi kokari a wannan shirin mu ba kowanne bangare damar bayyana abinda bincikensa ya nuna kan wannan lamarin, domin ba mai sauraro damar yanke hukumci bisa ga bayanan da aka samu.

Ga bayanin mahaifiyar wannan yaron Dr. Hannaru Ayuba, wadda likiciya ce a babban asibitin kasa dake Abuja, a hirarta da wakiliyarmu Madina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Kan batun cin zarafin Yaro Kurma PT1-10:00"