WASHINGTON, DC —
Shirin Domin Iyali na wannan makon yana dauke da rahoton kwamitin da gwamnan jihar Borno Kashim Shatimma ya kafa domin bincike zargin cin zarafin mata a wadansu gidajen yari. Sai dai bayan cikar wa'adin da aka dibar wa kwamitin ya gudunar da bincike, ya mika rahoto ba tare da kammala aikin ba, sabili da rashin samun hadin kai daga jami'an gidajen yarin, wadanda ake zargi da hannu a wannan lamarin, abinda gwamnan jihar yace ba zasu lamunta ba.
Har wa yau, akwai hira da shirin ya yi da Mallam Habibu Aliyu Kila, mahaifin Zainab Aliyu Dalibar da aka kulle a kasar Saudiya bisa zarginta da safarar miyagun kwayoyi bayan samun wata jakka a tashar jirgin saman da sunanta dauke da kwayar Tramadol.
Saurari cikakken shirin.
Facebook Forum