WASHINGTON, DC —
A makon jiya ne muka muka sami labarin cewa, tashin hankali da aka samu tsakanin miji da mata kan tarbiyartanta da 'yarsu ya janyo asarar ran maigidan. A cikin hirarsu da wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari, kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Abubakar Dan'inna ya bayyana cewa an kama matashin dan kimanin shekaru ashirin da biyar wanda ake zargin da kaurawa babanshin mafi a keya sau biyu da ake kyautata zaton shine ya zama ajalinsa.
Saurari shirin domin karin bayani kan wannan batun da kuma abinda masu fafatukar ceto 'yammatan Chibok ke neman ganin gwamnatin Najeriya tayi domin ganin an ceto dukan wadanda kungiyar Boko Haram ke rike da su, an kuma samar da tsaro a kasar.
Facebook Forum