Ranar Talata goma sha hudu ga watan Mayu Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren 'yammata daya tilo da kungiyar Boko haram take ci gaba da garkuwa da ita bayan sakin sauran Dalibar makarantar sakandaren Dapchi dari da hudu daga cikin dari da goma da ta sace ranar sha tara ga watan Fabrairu shekara ta dubu biyu da goma sha takwas da karfe biyar da rabi na yamma.
Tun daga wannan lokacin kungiyoyi da daidaikun jama'a a ciki da wajen Najeriya suke ta addu'oi tare da kira ga hukumomin Najeriya su dauki duk matakan da suka kamata na ceto ta. Kamar yadda aka yi bara lokacin da ta cika shekaru goma sha biyar a hannun kungiyar, a bana ma, an yi tarukan addu'oi da kuma kara jan hankalin duniya kan bukatar gaggauta ceto Leah. A cikin jawabin da ya gabatar a jami'ar Georgetown dake Washington DC, a nan Amurka, fitaccen marubucin nan da ya sami lambar yabo ta Nobel Wole Shoyinka ya yaba karfin halin Leah. Wole Shoyinka wanda ya rubuta wani maudu'i na musamman domin karrama Leah ya bayyana cewa, duk lokacin da ya koma yana karantawa sai ya yi hawaye domin bakin cikin halin da take ciki.
Shirin Domin Iyali ya sami zantawa da iyayen Leah ranar da ake bukin tunawa da haihuwarta . Ga abinda suke cewa.
Facebook Forum