Gobe Al'ummar Ghana Ke Zaben Shugaban Kasa

Nana Akufo Addo da madugun 'yan adawa da John Dramani Mahama shugaban Ghana mai ci yanzu

Idan Allah Ya kaimu gobe ne al'ummar Ghana zasu zabi wanda zai shugabanci kasar na wani tsawon shekaru hudu tsakanin shugaba mai ci yanzu John Daramani Mahama da madugun 'yan adawa Nana Akufo Addo

Yau ake kammala duk wani fafutikar neman zabe a kasar Ghana inda duk 'yan takaran suka yi gangami tare da yin alkawuran abubuwan da zasu yiwa al'ummar kasar.

Mai magana a madadin shugaban kasa yace gwamnatinsu tayi aiki ba tare da nuna wariya ba irin ta siyasa. Sun ba kowa ruwa da wasu ababen more rayuwa ba tare da yin la'akari da ko an zabesu ba ko ba'a yi ba. Zasu kuma cigaba da yin hankan da zara an mayar dasu karagar mulki.

Nana Akufo Addo dan hamayya da John Dramani Mahama shugaban kasa

Shi ko kakakin dan takarar jam'iyyar hamayya NPP ta madugun adawa Nana Akufo Addo, Mustapha Abdulhamid cewa yayi yana ganin mutanen Ghana suna da hurumin kawo canji a rayuwarsu sanadiyar zaben na gobe Laraba, bakwai ga watan Disamba din nan.

Abdulmahid yace siyasa ba addini ba ce saboda idan mutum ya mutu babu wanda zai tambayeshi jam'iyyar da yayi a duniya illa halinsa ya bishi. Ana siyasa domin samun anfani a duniya ne.

A nasa bangaren shugaban kasa John Dramani Mahaman yace duk da ayyukan da suka yi sun san Allah ne yake bada mulki. Allah ne yake nada mutum sarauta.

Nana Akufo Addo madugun adawa da John Dramani Mahama shugaban kasar Ghana mai ci yanzu

Saidai kuma kakakin madugun 'yan adawa ya fadawa mutane cewa wasu zasu ce Allah ne yake bada iko amma su tuna Allah baya ba azzalumai shugabanci.

Ga rahoton Baba Yakubu Makeri da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gobe Ake Zaben Shugaban Kasa A Kasar Ghana - 3' 03"