Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkaliyar Alkalan Ghana Ta Tabbarwa Al'ummar Kasar Kotu Zata Tunkari Kararrakin Zabe


Alkaliyar Alkalan Ghana Georgina Theodora Wood
Alkaliyar Alkalan Ghana Georgina Theodora Wood

Yayinda zaben kasar Ghana ke karatowa da kuma yawaitar arangama tsakanin magoya bayan 'yan takara alkaliyar alkalan kasar Georgina Theodora Wood ta ba kasar tabbacin cewa kotuna zasu yi aikinsu na tunkarar duk wata karar da aka gabatar game da zaben

Babar mai shari'ar tace kotu tayi damarar tunkarar kararrakin zabe da zara an gabatar dasu saboda hakkin tabbatar da an aikata gaskiya ba tare da nuna banbanci ba ya rataya ne a wuyan fannin shari'ar kasar kamar yadda kundun tsari ya tanada..

Bisa ga rantsuwar da suka yi zasu yi aikinsu tsakani da Allah. Tace sun himmatu da aikinsu. A matsayinsu na masu shiga tsakani zasu yi aikinsu da adalci domin kare muradu da manufofin dimokradiya.

Tace tana yiwuwa a samu rashin fahimta a lokacin zabe da bayan zabe. Idan hakan ya faru ba'a samu yadda ake so ba kotuna zasu magance duk irin wadannan matsalolin.

Alkaliyar Alkalan Ghanan tayi jawbinta ne a lokacin da take kaddamar da wasu takardu akan shigar da kararrakin zabe.

Su ma 'yan sandan kasar ta bakin DSP Imam Huseini sun shirya tsaf su tunkari kowace irin matsala ta taso lokacin zabe da bayan zaben.

Tambarin Rundunar 'Yansandan Ghana
Tambarin Rundunar 'Yansandan Ghana

Ga rahoton Baba Makeri da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG