Idan kuwa bata sauka ba, Ayariga yace zaben da za’ayi ran 7 ga watan na Disamba, ba zai kasance na adalci ba.
Sai dai kuma kungiyoyin sa-kai da dama na Ghana da kuma jami’an Hukumar Zaben kanta duk sunyi watsi da wannan kiran na Ayariga, inda suka ce shugabar ta jima tana aiwatar da dokokin zaben Ghana ba tareda nuna son kai ba.
A cikin makon nan ne dai Hukumar Zaben ta Ghana ta bayyana sunayen ‘yan takaran jam’iyyun siyasa bakwai da aka yardar wa shiga zaben shugaban kasan mai zuwa – sai dai shi Ayariga baya cikinsu, da yake Hukumar tace bai cika ka’ikdojin tsayawa ba.
Akan haka ne ya shigar da kara kotu inda kotun ta yarda da matsayinsa amma duk da haka, Hukumar zaben ta yanke shawarar hana mishi tsayawa zaben.