Wata gobara da ta tashi a wani ginin gidajen kwanan dalibai a Kenya ta kashe dalibai 18, yayin da wasu 27 kuma ke kwance a asibiti, tare da wasu yara 70 da ba’a san inda suke ba, a cewar mataimakin shugaban kasar a jiya Juma'a.
Shugaba William Ruto ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki inda za’a sassauto da tutocin kasar domin girmamawa ga yaran da suka mutu.
Mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua ya ce yara 86 ne kawai aka gani daga cikin yara sama da 150, ya kuma bukaci al’ummar yankin da watakila suka bai wa wasunsu mafaka da su taimaka su bayyana su.
Gachagua ya ce wani dalibi daya ya mutu a asibiti, kuma ya zuwa yanzu dalibai 37 sun hadu da iyayensu.
Ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar da ta tashi a daren Alhamis a makarantar firamare ta Hillside Edarasha da ke gundumar Nyeri, kamar yadda kakakin ‘yan sanda Resila Onyango ya bayyana. Makarantar tana da dalibai har zuwa ‘yan shekara 14.
Kwamishinan gundumar Nyeri Pius Murugu da ma’aikatar ilimi, sun ruwaito cewa gidan kwanan dalibai da gobarar ta kama na dauke da yara maza sama da 150 da ke tsakanin shekaru 10 zuwa 14.