Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Lambar NIN Kadai Ne Zasu Ci Gajiyar Buhun Shinkafa A Kan Naira Dubu 40 – Gwamnatin Najeriya


Shinkafa
Shinkafa

Sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan Naira dubu 40, mataki ne da gwamnatin tarayya ta dauka na zaftare farashin shinkafa ‘yar gwamnati da zimmar saukaka matsalar tsadar kayan abincin dake addabar Najeriya a halin yanzu.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ma’aikatan dake da lambar dan kasa ta NIN ne kadai za ta bari su sayi shinkafa yayin da ta kaddamar da shirinta na sayar da tan dubu 30 na casasshiyar shinkafar.

Yayin kaddamar da shirin, Ministan Harkokin Noma da Wadatar Abinci, Abubakar Kyari, yace an dauki wannan mataki ne domin magance rashin gaskiya, sannan wani yunkuri ne na sauke farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya.

Kyari, wanda ke wakiltar Shugaban Kasa Bola Tinubu, yace matakin zai tabbatar an sayarwa “ko wani mutum guda da buhun shinkafa daya.”

Ya kara da cewa, sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan Naira dubu 40, mataki ne da gwamnatin tarayya ta dauka na zaftare farashin shinkafa ‘yar gwamnati da zimmar saukaka matsalar tsadar kayan abincin dake addabar Najeriya a halin yanzu.

Ministan ya cigaba da cewa, gwamnati na sane da irin kalubalen da za a iya fuskanta yayin sayar da kayan abinci mai mahimmanci irin shinkafa, a wannan lokaci na tsanani don haka ta dauki mabambantan matakai, tare da bijiro da sharuda da tsare-tsare domin kamanta gaskiya da fadada shirin da kuma tabbatar da nasararsa.

"Matakan sun hada da tabbatar da cewa babu mutumin daya sayi fiye da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 guda daya, sauran sun hada tantance masu son cin gajiyar shirin ta hanyar amfani da dabarun tantancewa irinsu lambar dan kasa (NIN) da lambar waya domin magance mazambatan da zasu sayi shinkafar fiye da sau daya tare da tauyewa sauran ‘yan Najeriya hakkinsu”, a cewar Ministan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG