Gobara A Babbar Kasuwar Birnin Nairobi Ta Hallaka Mutane 15

Jami’ai a Kasar Kenya sun ce wata gobara ta auku a babbar kasuwar birnin Nairobi da safiyar yau Alhamis, har akalla mutane 15 sun mutu, wasu su 70 kuma sun jikkata.

Koda yake an iya kashe gobarar a kasuwar Gikomba, hukumomi sun nuna damuwa akan cewa ta yiwu wasu mutane sun makale a wani wuri cikin hayaki.

“Muna ta kokarin kawar da abubuwa, don abin da muke neman yi shine bude hanya, domin muna so mu tabbatar da cewa, ko a bangaren da ya kone babu mutane, a cewar wani mai magana da yawun gwamnatin kasar.

Jami’an kwana-kwana sun sha fesawa gobarar ruwa da sa’o'i bayan da gobarar ta tashi.