Girgizar Kasa Ta Afka Kusa Da Birnin New York

Birnin New York

Wani rahoton Hukumar Kula da Duwatsu (USGS) ta Amurka ya bayyana cewar, da safiyar Juma'ar nan, wata girgizar kasa ta afkawa yankin arewa maso gabashin birnin New York mai yawan jama'a, inda mazauna yankin suka bada labarin jin motsin kasa, al'amarin da basu saba ji ba.

WASHINGTON DC - Hukumar ta bada rahoton samun girgizar kasa mai karfin maki 4.8 a ma'aunin richter da misalin karfe 10 da mintuna 23 na safiyar yau Juma'a kusa da yankunan Lebanon da New Jersey ko tazarar mil 45 yamma da birnin New York ko mil 50 arewa da Philadelphia.

Alkaluman hukumar sun nuna cewar, me yiyuwa fiye da mutum milyan 42 sun ji motsawar kasar.

Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin New York ta wallafa a shafinta na sada zumunta mintuna 30 bayan samun girgizar kasar cewar, bata samu rahoton barna ko jikkata a wani sashe na birnin ba.

A jawabinsa game da girgizar kasar, Magajin Garin Birnin New York, Eric Adams, wanda mai magana da yawunsa, Fabien Levy ya wakilta yace, "a yayin da muke dakon samun rahoton irin barnar da girgizar kasar ta haddasa, har yanzu muna tattara bayanai akan tasirinta.

Al'umomin da suke zaune a yankunan Baltimore da Philadelphia da Connecticut da sauran sassan yankin arewa maso gabashin Amurka sun bada rahoton jin motsin kasar.

An jiyo motsawar kasar tsawon dakikoki daga nisan fiye da mil 200 kusa da kan iyakokin jihohin massachusetts da new hampshire.

AP