ACCRA, GHANA - Kudaden da Ghana ke sayo mai da su a kasashen waje sun tashi daga dala miliyan dari biyu da hamsin a watan Janairun bana zuwa miliyan dari hudu da hamsin a watan Mayu.
Babban bankin kasar da ke fama da matsalar karancin dala ya dage kan matsayinsa na cewa miliyan dari kadai kasar za ta iya samarwa kamfanonin da ke da alhakin rarraba mai a Ghana domin sayo mai daga kasashen waje a yanzu.
Dakta Kwame Sarkodie, mai sharhi kan harkar man fetur kuma malami a jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah da ke Ghana, ya tabbatar da cewa Ghana za ta tsunduma cikin matsalar karancin mai nan ba da jimawa ba saboda ana fuskantar cikas wurin shigo da mai kasar, abinda kuma ya alakanta da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.
Mallam Abu Naeem Afandi, mai sharhi ne a kan harkar tattalin arziki a Ghana, ya ce ko shakka babu karancin dalar Amurka a kasar zai haddasa matsaloli da dama a nan gaba saboda idan mutum na dauke da kudin sidi da yawa da wuya ya samu dalar Amurka, kuma dole sai da dalar ake kasuwancin mai a kasashen waje.
Sai dai mai magana da yawun hukumar man fetur a Ghana Malam Muhamad Kudus, ya ce Ghana na da man da za ta yi amfani da shi har zuwa wata daya, a don haka kada al’umma su yi fargaba.
"Ya kamata Ghana ta kafa babbar masana’antar mai saboda ta na da albarkatun mai, sannan ta kuma inganta matatar mai ta Tema Oil Refinery, hakan zai maida kasar mai sayar da mai maimakon mai sayo mai daga kasashen waje," a cewar Sarkodie.
Tun daga watan Janairun shekarar nan ta 2022 aka fara fuskantar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, abinda aka alakanta tsadar mai da kuma faduwar darajar kudin sidi bisa dalar Amurka, da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5