ACCRA, GHANA - Yayin da yake gabatar da jawabi daga taron ci gaban kasashen Turai (EDD) a Brussels babban birnin kasar Belgium, shugaban ya ce "Bankin Duniya ya fada masu cewa, yawan rikici da ke aukuwa ya yi sanadiyyar samun karuwar talakawa a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.
Ya kara da cewa, adadin zai haura daga miliyan dari hudu da sha uku (miliyan 413) zuwa miliyan dari hudu da sittin da uku (miliyan 463) a wannan shekara, wato an samu karuwar talakawa miliyan hamsin (miliyan 50).
Ya bukaci Tarayyar Turai da su kara himma wajen taimaka wa kasashe masu tasowa don jure barnar da annobar cutar coronavirus tayi. Da kuma dagulewar tattalin arzikin kasashe masu tasowar, sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.
a cewarsa kamar yadda rahoton na baya-bayan ya fito daga Majalisar Dinkin Duniya cewa kashi saba'in (70%) na tattalin arzikin Afirka na cikin saka maiwiya sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.
Shugaban ya kuma tabo alakar da ke tsakanin Afirka da Tarayyar Turai, wanda a cewarsa, kamata ya yi ta zama sanadin kara tabbatar da cewa Afirka ta samu taimakon da take bukata, musamman a wannan lokaci da take cikin mawuyacin hali.
Mallam Hamza Attijani masani akan tattalin arziki ya ce bai kamata kasashen Afirka su dinga zuba wa Tarayyar Turai ido wajen karban rance a duk lokacin da suke cikin yanayin tabarbarewar tattalin arziki ba, lokaci yayi da ya kamata su gina kansu ta yadda zasu dinga dogaro da kansu.
Daga karshe shugaban na Ghana yayi kira ga shugabannnin kasashen Afirka da su hada kai suyi aiki tare don cimma burinmsu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hawa AbdulKarim: